Skip to main content

Posts

Showing posts from November, 2019

MARIGAYA SHAIKH JA'AFAR DA SHAIKH ALBANI ZARIA

A kullum ana samun Guluwwi ne a inda jahilci ya hadu da zafin kai da wautar tunani. Wannan ya sa za ka samu wadannan abubuwa su ne sababi na Guluwwi a Kafirtawa da Guluwwi a Bidi'antarwa. A cikin kwanakin nan ana tattauna wasu sababbin maganganu da suka bayyana na wani daga cikin 'Yan Kungiyar Salafiyyun masu Guluwwi a Bidi'antarwa na bidi'antar da Marigayi Shaikh Ja'afar da Shaikh Albani Zari'a, da kuma wasu Malaman da a yanzu suna da rai. Alhali in ka nazarci hukuncin da wadannan 'Yan Kungiyar Salafiyyun din suka yi ga wadannan Malamai za ka ga kawai ya ginu ne a kan jahilci da zafin kai. Dalili a kan haka, matasan sun jahilci sabuban Bidi'a, da halin da ake bidi'antarwa, da yanayin mutumin da ake bidi'antarwa. Saboda ba kowane wanda aka samu wata dabi'a ta 'Yan Bidi'a a tare da shi yake zama Dan Bidi'a ba. Za ka iya samun mutum da wata dabi'a ta Khawarijawa amma kuma bai zama Bakhawarije ba. Shaikhul Islami ya ce:...

MAGANIN KARYA SIHIRI(HAYAKI)

 Alhamdulillah kamar yadda mukai Alkawarin zamu kawo maganin wanda yake karya sihiri ko jifa,ko sammu Allah ya nufa yau mun cika shi. Kuma shi wannan na hayaki ne wanda mutum zai hada ya rika zuba shi akan garwashi yana amfami dashi,yadda abun yake kuma shine..... ABINDA ZAA NEMA. 1. Kaikayi koma kan mashekiya 2. Garin kusdul hindi 3. Garin haltit Zaa hade wannan waje daya,sai a rika diban kadan ana zubawa akan wuta mara lafiya ya rika shakar hayakin. Idan kuma don kariya zaai kawai sai a saka a daki ko a cikin gida. Wallahu a'alamu Abin sadaqa ayiwa Annabi sallallahu Alaihi wasallam Salati. LIKE AND SHARE.

Yadda Ake Yin Sallar Jana'iza

'YAN-UWA mafi yawancinmu, muna yin Sallar Jana'iza amma kuma ba mu san abinda ake fada a cikin kowacce Kabbara ba. Dan haka ya sa muka ga cewa yana da kyau mu ware wani lokaci na musamman, Domin fahimtar da mu yadda ake yin sallar Jana'za. 'YAN-UWA ita dai Sallar janai'za, tana da babban lada, ga wanda ya aikata ta kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya koyar, dan haka yana da kyau, mu tsaya mu koya. Kamar yadda na ce, sallar jana'za tana da kabbarori guda hudu ne kawai kuma kowacce Kabbara da abin da ake fada a cikinta. 1. KABBARA TA FARKO ana karanta {suraul-fatiha} ne kawai, banda wata sura, ko wata a'ya. 2. KABBARA TA BIYU ana karanta Salatin Annabi ba wani salati na daban ba. 3. KABBARA TA UKU ana yin addu'a ga wanda ya mutu mace ko namiji. 4. KABBARA TA HUDU za ka yi addu'a ne ga sauran al'ummar Musulmi Wadanda suke Raye da matattu. DAN UWA KANA GAMAWA sai ka jira Liman ya yi sallama. Ita kuma sallamar guda daya ce tak! ...

DUBIYAR MARASSA LAFIYA....

Kungiyar Izala ta fara gudanar da aikin duba majinyata kyauta a garin Azare jihar Bauchi. Cikin shirye-shiyenta na gudanar da wa'azin kasa a garin Azare dake jihar Bauchi, Kungiyar Izala ta kasa ta fara gudanar da shirinta na duba majinyata kyauta. Shirin wanda aka bude a safiyar yau laraba karkashin jagorancin Alhaji Abba Yahaya (National Secretary FAG of JIBWIS) da Alhaji Bello Abubakar Maradun da Malam Usman Idris Funtua tuni aka fara aiwatar dashi ga majinyata maza da mata. Yayin da yake jawabi lokacin bude shirin, shugaban Kungiyar Izala ta jihar Bauchi Imam Engr. Alhaji Muhammad Inuwa Dan'asabe ya bayyana Jin dadinsa dangane da sanya wannan gagarumin aiki a wannan jiha kana ya tabbatar da goyon bayansa ga masu aiwatar da wannan aiki domin samun nasara daga farkonsa har karshe. Shima jagoran shirin a matakin kasa Matawallen Diggi wanda yasamu wakilcin Dr. Abba Yahaya ya nanata aniyarsu na gabatar da ayyukan bada taimako ga  majinyata ta hanyar yin kaho (Hijama) da ...

USULUS SALAFIYYA

MU SAKATA DA WANNAN

Wani mutumne yaje gurin wani cin abinci. yana zaune sai yaga wani mutum shima yazo ya zauna acan daga gefa . Tofa sai yaga wani mutum yazo ya durkusa yace Ranka ya Dade matatace akai kaita asibiti ance nakawo kudi kuma bani dashi . Sai ya dauko check ya bashi yace ga one million nan saimutumin nan ya karba yana tamurna yayi godiya ya tafi. . Sai can wani mutuminma yakara zuwa ya fadi bukatarsa shima aka bashi check na million aa wannan mutum du yana kallo can can shima sai ya faratunanin shikuma mai zaice ya tashi . da sauri Dan kar wani ya rigashi ko alhaji ya tafi sai Yai Sauri Yaje yana tsuggunawa sai yaji wani yace . malam karfa kashigar mana film saboda kunya. dai wannan mutum baice komaiba��sumsumsum ya bar gurin ko abincin bai karasa cinyewaba ya FIta daga gun lol Banda dariya....

Adam A Zango

Jarumi Adam Zango Yasake Martani Me Zafi Akan Ficewarsa Daga KannyWood.