Kungiyar Izala ta fara gudanar da aikin duba majinyata kyauta a garin Azare jihar Bauchi.
Cikin shirye-shiyenta na gudanar da wa'azin kasa a garin Azare dake jihar Bauchi, Kungiyar Izala ta kasa ta fara gudanar da shirinta na duba majinyata kyauta.
Shirin wanda aka bude a safiyar yau laraba karkashin jagorancin Alhaji Abba Yahaya (National Secretary FAG of JIBWIS) da Alhaji Bello Abubakar Maradun da Malam Usman Idris Funtua tuni aka fara aiwatar dashi ga majinyata maza da mata.
Yayin da yake jawabi lokacin bude shirin, shugaban Kungiyar Izala ta jihar Bauchi Imam Engr. Alhaji Muhammad Inuwa Dan'asabe ya bayyana Jin dadinsa dangane da sanya wannan gagarumin aiki a wannan jiha kana ya tabbatar da goyon bayansa ga masu aiwatar da wannan aiki domin samun nasara daga farkonsa har karshe.
Shima jagoran shirin a matakin kasa Matawallen Diggi wanda yasamu wakilcin Dr. Abba Yahaya ya nanata aniyarsu na gabatar da ayyukan bada taimako ga majinyata ta hanyar yin kaho (Hijama) da kuma binciken lafiya na bai daya (medical check up) tun daga yau Laraba har zuwa ranar Asabar.
Daga bisani shugaban ya zagaya masaukai da aka tanada wa baki mahalarta wannan gagarumin taro inda ya samu damar duba sama da masaukai guda goma. Tuni dai-daikun jama'a suka fara bada gudumowansu na gidaje da alkawarin abinci domin tarayya cikin lada.
Cikin 'yan tawagan shugaban harda Shugaban Majalisar malamai ta jiha Assheikh Sulaiman Yusuf Bashir da Daraktan Agaji Alhaji Umar Jabir da Mataimakin sakataren kungiya ta jiha Alhaji Ilyasu Danjuma Bandas sai Sakataren Majalisar malami Mal Hamza Muhd (SMA) sai SIO na jiha Alhaji Abdullahi Tambari da kuma Daraktan Social Media na jiha Ustaz Muhammad Nasir Abdullahi.
Dafatan Allah ya sanya albarka ma wannan muhimmin aiki na alkhairi.
JIBWIS Social Media
Bauchi state Directorate
21
/11/2019

Comments
Post a Comment