Skip to main content

USULUS SALAFIYYA

Usulus Salafiyya su ne tushe da ginshikan da Salafiyya ta hakika ta ginu a kansu. Kuma kowane asali za ka samu dalili a kansa karara a cikin Alkur'ani ko Sunnar Manzon Allah (saw), kuma Salaf Magaba suka yi Ijma'i a kansa.

Wadannan ginshikai kuwa su ne kamar haka:
(1) Bin Alkur'ani da Sunna da girmama su da sallama musu, da daukar Addini daga gare su.
(2) Riko da fahimtar Salaf Magabata da bin Ijma'insu.
  • (3) Yin imani da Rakunnan Imani guda shida:
a) Babban tushensu shi ne Imani da Allah, ta hanyar kadaita shi a Rububiyyarsa, da kadaita shi a bauta, da tabbatar da Sunayensa da Siffofinsa da suka zo cikin Alkur'ani da Sunna, ba tare da Tawili ko kamantawa ko korewa ba.
b) Imani da Mala'ikun Allah, da Littatafansa, da Manzanninsa, da Ranar karshe.
c) Imani da Kaddara na alherinsa da na sharrinsa.
(4) Imani magana ne da aiki, yana karuwa, yana raguwa da aikata sabo.
(5) Nisantar kafirta Musulmi a kan aikata sabo, sai dai in ya aikata abin da yake warware Muslunci.
(6) Sauraro da da'a ma shugabannin Musulmai ko da azzalumai ne, matukar ba su yi umurni da sabon Allah ba.
(7) Rashin yin tawaye wa shugabannin Musulmai idan sun aikata sabo matukar bai kai matsayin kafirci ba.
(8) Girmama Sahabbai, da ganin falalarsu da wanke zuciya da tsare harshe a kansu, da yi musu addu'a ta samun yardar Allah.
(9) Son Alul Baiti da Matan Annabi (saw) da jibintarsu da ganin falalarsu.
(10) Haduwa a kan Bin Sunna da nesantar rarrabuwa.
(11) Nesantar Bidi'a da 'Yan Bidi'a.

Wadannan ginshikai, manyan Malaman Sunna sun tabbaar da su cikin littatafansu, musamman:
1- Usulus Sunna, da aka ruwaito daga Imamu Ahmad bn Hanbal.
2- Al-Aqidatut Dahawiyya, na Imamu Dahawiy.
3- Al-Aqidatul Wasidiyyah, na Shaikhul Islami Ibn Taimiyya.

Don haka, duk wani abu da babu shi karara a cikin Alkur'ani da Sunna, kuma ba ya cikin wadannan littatafai guda uku da muka ambata, to babu yadda za a yi ya zama Asali daga cikin "Usulus Salafiyya ta hakika", saboda daga Alkur'ani da Sunna ake dauko su.

Da wannan za ka san kuskuren 'Yan Kungiyar Salafiyyun, na kirkiran wasu abubuwa da sanya su matsayin "Usulus Salafiyya", kamar:
1- "Imtihani da Ashkhaas", wato yin jarabawa wa mutane da Shaikh wane, da wane.
2- Inkarin Muwazana.
3- Al- Jarhu wat Ta'adeel, da makamantansu.

Comments

Popular posts from this blog

MAGANIN KARYA SIHIRI(HAYAKI)

 Alhamdulillah kamar yadda mukai Alkawarin zamu kawo maganin wanda yake karya sihiri ko jifa,ko sammu Allah ya nufa yau mun cika shi. Kuma shi wannan na hayaki ne wanda mutum zai hada ya rika zuba shi akan garwashi yana amfami dashi,yadda abun yake kuma shine..... ABINDA ZAA NEMA. 1. Kaikayi koma kan mashekiya 2. Garin kusdul hindi 3. Garin haltit Zaa hade wannan waje daya,sai a rika diban kadan ana zubawa akan wuta mara lafiya ya rika shakar hayakin. Idan kuma don kariya zaai kawai sai a saka a daki ko a cikin gida. Wallahu a'alamu Abin sadaqa ayiwa Annabi sallallahu Alaihi wasallam Salati. LIKE AND SHARE.

ASALIN RUBUTUN HAUSAR BOKO KASHI Na ( 2 )

Zuriyar Harshen Hausa Masana ilimin harsuna sun karkasa harsunan duniya zuriya-zuriya. Kowane harshe na duniyar mutane dole da rukunin da yake. A rukunin da ya fito nan ake kirdadon tushensa da tushen masu magana da shi. Masana ilimin harshe sun ce: Hausa harshe ne daga cikin  zuriyar harsunan Chadi, waɗanda sun kai fiye da harsuna ɗari da ake magana da su a Arewacin Najeriya da Arewacin Kamaru da kuma tsakiyar Chadi.” Daga cikin harsuna iyalan Chadi, Hausa ta fi kowane bazuwa da yawan jama’a da karɓuwa da mamaye ƙasa. Daga cikin fahimtar sanin asalin harshe shi ne a san tarihinsa. Babban muhimmin abu shi ne gano dangantakar harshe da sauran harsunan da suke zuriya/iyali ɗaya. Babu makawa ga mai son sanin tushen Hausa ya yi ƙwaƙƙwaran nazarin harsuna iyalan Chadi. A tsarin ilimin harsuna an ce: Idan aka ce harshe (kaza) ɗan iyalan gungun harsuna (kaza) ne, ana son a tabbatar da cewa, a da can baya harshe ɗaya ne kacal daga gare shi ne sauran harsunan zuriyarsa suka tsir...

MARIGAYA SHAIKH JA'AFAR DA SHAIKH ALBANI ZARIA

A kullum ana samun Guluwwi ne a inda jahilci ya hadu da zafin kai da wautar tunani. Wannan ya sa za ka samu wadannan abubuwa su ne sababi na Guluwwi a Kafirtawa da Guluwwi a Bidi'antarwa. A cikin kwanakin nan ana tattauna wasu sababbin maganganu da suka bayyana na wani daga cikin 'Yan Kungiyar Salafiyyun masu Guluwwi a Bidi'antarwa na bidi'antar da Marigayi Shaikh Ja'afar da Shaikh Albani Zari'a, da kuma wasu Malaman da a yanzu suna da rai. Alhali in ka nazarci hukuncin da wadannan 'Yan Kungiyar Salafiyyun din suka yi ga wadannan Malamai za ka ga kawai ya ginu ne a kan jahilci da zafin kai. Dalili a kan haka, matasan sun jahilci sabuban Bidi'a, da halin da ake bidi'antarwa, da yanayin mutumin da ake bidi'antarwa. Saboda ba kowane wanda aka samu wata dabi'a ta 'Yan Bidi'a a tare da shi yake zama Dan Bidi'a ba. Za ka iya samun mutum da wata dabi'a ta Khawarijawa amma kuma bai zama Bakhawarije ba. Shaikhul Islami ya ce:...