A kullum ana samun Guluwwi ne a inda jahilci ya hadu da zafin kai da wautar tunani. Wannan ya sa za ka samu wadannan abubuwa su ne sababi na Guluwwi a Kafirtawa da Guluwwi a Bidi'antarwa.
A cikin kwanakin nan ana tattauna wasu sababbin maganganu da suka bayyana na wani daga cikin 'Yan Kungiyar Salafiyyun masu Guluwwi a Bidi'antarwa na bidi'antar da Marigayi Shaikh Ja'afar da Shaikh Albani Zari'a, da kuma wasu Malaman da a yanzu suna da rai. Alhali in ka nazarci hukuncin da wadannan 'Yan Kungiyar Salafiyyun din suka yi ga wadannan Malamai za ka ga kawai ya ginu ne a kan jahilci da zafin kai.
Dalili a kan haka, matasan sun jahilci sabuban Bidi'a, da halin da ake bidi'antarwa, da yanayin mutumin da ake bidi'antarwa. Saboda ba kowane wanda aka samu wata dabi'a ta 'Yan Bidi'a a tare da shi yake zama Dan Bidi'a ba. Za ka iya samun mutum da wata dabi'a ta Khawarijawa amma kuma bai zama Bakhawarije ba.
Shaikhul Islami ya ce:
إن كثيرا من النساك والعباد والزهاد قد يكون فيه شعبة من الخوارج وإن كان مخالفا لهم في شعب أخرى
الاستقامة (1/ 260)
"Da yawa daga cikin masu Nusuki da Ibada da Zuhudu zai iya kasancewa mutum yana da hali guda na Khawarijawa, alhali kuma ya kasance ya saba musu a wasu rassan daban".
Kamar yadda mutum zai iya kasancewa yana da "shu'uba" ta Munafurci amma bai zama Munafuki ba, haka idan mutum yana da wata dabi'a ta 'Yan Bidi'a ba lallai ne ya zama Dan Bidi'a ba. Zai iya zama mai sabo ko mai kuskure da Allah zai gafarta masa kuskuren nasa saboda Tawili.
Sa'annan kuma, lamarin Kasarmu Nigeria, wajen kasancewarta Kasar Muslunci ko ta Kafirci, abu ne da yake iya daukar Ijtihadi da Tawili. A irin wannan hali yaushe za ka yi hukunci da Bidi'a ga Malamin da yake wa'azi mai zafi ga Gomnatin Obasanjo ko ta Jonathan?!
Shaikhul Islami ya ce:
إن المتأول المعذور لا يفسق؛ بل ولا يأثم.
مجموع الفتاوى (32/ 135)
"Lallai Mai Tawili Mai uzuri ba a fasikantar da shi, kai, ba ma zai samu zunubi ba".
A wani waje kuma ya ce:
والتأويل يمنع الفسوق.
مجموع الفتاوى (3/ 230)
"Tawili yana hana a fasikantar da mutum".
Bidi'antarwa yana cikin fasikantarwa ne, saboda Bidi'a da ake Bidi'antar da mutum da ita, imma ta zama ta Kafirci ce ko kuma ta Fasikanci.
-Wai- a hakan ne suke ikirarin sun je sun yi musu Nasiha, sun tsayar musu da hujja, sun yaye musu shubuha!
Yaushe Jahili zai yaye shubuha wa Malami?!
Sa'annan ka je inkari da zafin kai, yaushe inkari da zafin kai ya taba zama Nasiha?!
Sa'annan -wai- sun je sun yi fatawa a kan su Malam Ja'afar, an ce: 'Yan Bidi'a ne. To in fatawar gaskiya kake so ka yi a kan Malam Ja'afar, sai ka yi tafawar wa Shaikh Muh'd Zarban Al-Gamidiy, don shi ne ya san Malam Ja'afar. Amma duk wata fatawa da mutum zai yi a wajen wanda bai san Malam Ja'afar ba, sunanta fatawa gama gari, ba hukunci ce a kan Malam Ja'afar ba. Malaman da suka san Malam Ja'afar da Albaniy Zaria da Da'awarsu su ne za su iya yanke hukunci a kansu ba wani a can gefe da bai sansu ba.
Don haka in ka zo mana da wata fatawa daga malamin da bai sansu ba to sai mu ce: karya kake yi, kai ne ka yanke musu hukunci ba wancan Malamin ba, kai kuma mun san ba ka kai wannan matsayin ba.
Hatta Malaminmu Shaikh Dr. Abubakar Sani Birnin Kudu da suke ta kokarin cusuwa masa, kwata - kwata ba ya goyon bayansu a kan wannan Manhaji na Guluwwi da Zafin kai da Kungiyanci da suke yi da sunan Salafiyya. Wallahi da a ce: za su yi aiki da abin da yake gaya musu da ba su kama wannar hanya ba. Saboda abin da Malam yake fada musu shi ne; shi ba ya tuhumar Aqidar kowa daga cikin wadannan Malaman Sunnan da su suke Bidi'antarwa. Har yake ce musu: Na sani duk maganar taku saboda "Al-Muntada" ce, alhali duk cikin Muntadan babu wani da ya kai wadannan Malaman Ilimi da har za su yi musu barbarar mummunar Aqida.
Saboda haka, duk wanda ya san Manhajin Malaminmu Dr. Birnin Kudu ya san cewa; ba ya tare da wannan zafin kai. Kai, hasali ma 'yan wannar kungiyar ta Salafiyyun, a kullum sukan Malaman Dr. Birnin Kudun suke yi, suna kiransu da sunan "Mumayyi'ah", -wai- masu narkar da Salafiyya su lalata ta. Wato irin su Shaikh Saleh Al-Suhaimiy, Shaikh Ibrahim Al-Ruhailiy. Kai, kusan suna daukar Malaman Department din su Malam Birnin Kudu na Aqida a Jami'ar Madina gaba daya a matsayin "Mumayyi'ah" ba Salafiyyun ba, don kawai sun barranta daga wannan Manhaji na Guluwwin da sunan Jarhi da Ta'adili.
Ai mun ga abin da ya faru a bara bayan an yi wani "Mu'utamar" a kan Bayanin Asalin Ahlus Sunna wal Jama'a, wanda aka yi a Kasar Kuwait, wanda shi Dr. Birnin Kudu ya halarci taron, wanda ya gudana karkashin jagorancin su Shaikh Al-Suhaimiy da Muftin Mauritania, inda suka fito suna ta suka iri - iri.
Saboda haka su wadannan 'Yan Kungiyar Salafiyyun masu Guluwwi a Bidi'antarwa na Nigeria, kawai tun tuni suna ta neman Malami ne wanda ya yi karatu a Madina ido a rufe shi ya sa suke ta cusuwa ma Dr. Birnin Kudu, alhali Manhajin Da'awarsu ya yi hanun riga da nasa Manhajin. Saboda Wallahi in da za su bi fadakarwar da yake yi musu da tuni sun yi watsi da wannan Manhaji na Kungiyanci da sunan Salafiyya.
Comments
Post a Comment