Zuriyar Harshen Hausa Masana ilimin harsuna sun karkasa harsunan duniya zuriya-zuriya. Kowane harshe na duniyar mutane dole da rukunin da yake. A rukunin da ya fito nan ake kirdadon tushensa da tushen masu magana da shi. Masana ilimin harshe sun ce: Hausa harshe ne daga cikin zuriyar harsunan Chadi, waɗanda sun kai fiye da harsuna ɗari da ake magana da su a Arewacin Najeriya da Arewacin Kamaru da kuma tsakiyar Chadi.” Daga cikin harsuna iyalan Chadi, Hausa ta fi kowane bazuwa da yawan jama’a da karɓuwa da mamaye ƙasa. Daga cikin fahimtar sanin asalin harshe shi ne a san tarihinsa. Babban muhimmin abu shi ne gano dangantakar harshe da sauran harsunan da suke zuriya/iyali ɗaya. Babu makawa ga mai son sanin tushen Hausa ya yi ƙwaƙƙwaran nazarin harsuna iyalan Chadi. A tsarin ilimin harsuna an ce: Idan aka ce harshe (kaza) ɗan iyalan gungun harsuna (kaza) ne, ana son a tabbatar da cewa, a da can baya harshe ɗaya ne kacal daga gare shi ne sauran harsunan zuriyarsa suka tsir...