Skip to main content

ASALIN RUBUTUN HAUSAR BOKO KASHI Na ( 2 )

Zuriyar Harshen Hausa

Masana ilimin harsuna sun karkasa harsunan duniya zuriya-zuriya. Kowane harshe na duniyar mutane dole da rukunin da yake. A rukunin da ya fito nan ake kirdadon tushensa da tushen masu magana da shi. Masana ilimin harshe sun ce:

Hausa harshe ne daga cikin  zuriyar harsunan Chadi, waɗanda sun kai fiye da harsuna ɗari da ake magana da su a Arewacin Najeriya da Arewacin Kamaru da kuma tsakiyar Chadi.”

Daga cikin harsuna iyalan Chadi, Hausa ta fi kowane bazuwa da yawan jama’a da karɓuwa da mamaye ƙasa. Daga cikin fahimtar sanin asalin harshe shi ne a san tarihinsa. Babban muhimmin abu shi ne gano dangantakar harshe da sauran harsunan da suke zuriya/iyali ɗaya. Babu makawa ga mai son sanin tushen Hausa ya yi ƙwaƙƙwaran nazarin harsuna iyalan Chadi. A tsarin ilimin harsuna an ce:

Idan aka ce harshe (kaza) ɗan iyalan gungun harsuna (kaza) ne, ana son a tabbatar da cewa, a da can baya harshe ɗaya ne kacal daga gare shi ne sauran harsunan zuriyarsa suka tsira.”

Abubuwan da ke sa masu magana da harshe su warwatse, harshen ya ragaice, sun haɗa da yaƙe-yaƙe da yunwa da annoba da mulkin mallaka da kuma buƙatar ɗan Adam ta sauya mazauni ko babu dalili. Idan aka duba, sojojin Romawa a kai da kawonsu na yaƙe-yaƙe suka tsirar da harshen su Spanish da French da Italiya da Portuguese da kuma harshen Latin. Paul Newman (1977) ya karkasa harsunan iyalin Chadi kamar haka

Chadic

‘Wastern Chadic”

A.Hausa da Bale da Kare-Kare da Kanakuru da Angas da Sur da kuma Ron.

B.Bade da Ngizim da Warji da Miya da Sayanci

“Central Chadic”

A.Tera da Bura da Margi da Higi da Mandara da Gisiga da Daba da kuma Ɓacama

Katoko da Musgu da Gidar
“East Chadic”

A.Kera da Samuai da Tumak da kuma Lele

B.Dangala da Mokuku da Sokoro da Masa da Zima sai kuma Lame.

Tun fil’azal Hausa na da tushe na farko cikin harsunan iyalan Chadi. Batun rashin asalin da wadansu ke faɗa bai taso  ba. Yadda masana harshe suka daddagi wannan matsalar ba tare da duba zuwa ga wasu muhimman makaman al’ada ba, shi ya haddasa hazo a tarihin aka shiga ƙila-wa-ƙala.

Daddale  hasashe-hasashen masana

Daga cikin makaman da masana suke amfani da su akwai na Adabin Baka, akwai na Ilimin Harsuna, akwai na Tarihi, akwai na Siyasa, akwai na Walwala. Lange da takwarorinsa na Daura sun tafi a kan ingancin Tarihihin Bayajida. Paul Newman da Rusell G. Schuch da Greenburgh da takwarorinsu sun tafi a kan mai da hankali ga zuriyar Afirka a ƙyallaro ina Hausa ta fito. 

Hambali Junju da makamin harshe ya yi amfanin amma a wajen ƙasar Hausa (Masar). Ɗanmasanin Kano, ya haɗo adabi da al’ada, amma a wajen ƙasar Hausa (Habasha).  Muhammadu Uba Adamu a sabon aikinsa, tarihi da al’ada ya sa gaba ya je Masar ya yada zango. Mahadi Adamu a makamin tarihinsa a ƙasar Hausa ta yau ya tsaya, kuma a nan yake ganin mun tsira.

A taciyar ƙunshiyar fahimtocinsu, akwai masu ganin a tarihin asalin Hausawa da harshensu dole sai an fita wajen ƙasar Hausa. kashi na biyu na ganin, a dai tsaya a kai na hannu gida, kafin a dawo a kama na dawa, wato a sussuka ɗakar daka shiƙar ɗaka, asalin Bahaushe na nan cikin ƙasar Hausa. Su duka biyu, da sun ba al’ada muhimmanci ga sanin mai ita da ra’ayoyinsu sun yi canjaras a mahaɗa  ɗaya.

Biri ya yi kama da mutum

Manyan daulolin ƙasar Hausa wata babbar madafa ce, idan ana zancen asalin Bahaushe da harshensa. Idan ana batu a kan Bahaushe, su ne Hausa. Duk da haka, a tarihin kafuwar wasu daga cikin daulolin yana ƙoƙarin nuna daga wajen ƙasar Hausa waɗanda suka kafa su suka zo. Ga ɗan abin da ya kyautu a harara daga bakin masu abu:

Daular Gobir: Abubuwan da aka samo  daga bakunan Gobirawa da masu nazarin tarihinsu suna nuna daga  Masar ko Iraƙi ko Makka suka fito. Riwayoyin sun kai biyar.

Daular Zamfara: A tarihihi suna cikin Banza Bakwai, daga cikin daulolin ita kaɗai aka samu cewa, taron dangi ne na Hausawa da sauran ƙabilu ’yan gida.

Daular Kano: Ga alama, tussan kafa tarihinta daga cikin gida ne, amma dogaro ga waƙar Bagauda da masu ruwaito tarihinta suka yi yana nuna ba daga nan suka tsira ba.

Daular Zazzau: Masana tarihi na danganta asalinta da sarautun mata ko Sarauniya Amina. Duk da haka, masarautar daular ta gamin-gambiza ce.

Daular Kabi (Kebbi): A tarihihin suna iƙirari da Ka’aba. Idan aka bi salsalar Kanta da ya ɓalle daga sojojin Askiyya tushenta wajen ƙasar Hausa zai kasance.

Daular Katsina: Bayan tarihihin Bayajida da ya mamaye Daura, birnin Katsina ya keɓantu daga ƙurar guguwar cewa, daga wajen ƙasar Katsina waɗanda suka kafa ta suka fito.

Bincike ya nuna ba dukkan daulolin ƙasar Hausa suka aminta daga wajen ƙasar Hausa suka zo suka kafa ƙasar Hausa ba. A ko’ina suka fito daga cikin Nahiyar Afirka da addininsu suna da makusanciyar dangantaka. Idan aka bi fassarar masana ilimin harsuna ’yan iyali ɗaya ne. Ra’ayoyi da ƙoƙarin danganta Bahaushe daga wurare masu nisa, musamman Gabas da Yamma, da Gabas Mai nisa, na masu ra’ayin wariyar launin fata ne da ganin ’yan Afirka ba su da tushe.

Dole uwar na ki

Tunanin wannan aiki a nan shi ne, sai an sake lale an koma ga tushen al’amari. Ra’ayoyin cewa daga wajen duniyar Afirka Bahaushe ya ƙaurato ya zo ya kafa ƙasar Hausa raini ne da kushe baƙar fata na ’yan mu kaɗai muka iya. Wannan tunanin nake son a yi tonon silili a ga daga ina ake kirdadon mutum ya fara zama a duniya? Wane ne mutum na farko a duniya?  Yaya siffarsa take ta launisa da zatinsa? A tunanin Farfesa Dawin daga birai aka fara, har aka kawo ga mutum na yau. Duk da ɗimbin raunin  da ke ga wannan ra’ayi, za mu so mu ji, daga Dawin da ’yan rakiyarsa, shi birin daga wace nahiya ya fito? Ga yadda sahabban Dawin ke hangen amsoshin waɗannan tambayoyin:

Comments

Popular posts from this blog

MAGANIN KARYA SIHIRI(HAYAKI)

 Alhamdulillah kamar yadda mukai Alkawarin zamu kawo maganin wanda yake karya sihiri ko jifa,ko sammu Allah ya nufa yau mun cika shi. Kuma shi wannan na hayaki ne wanda mutum zai hada ya rika zuba shi akan garwashi yana amfami dashi,yadda abun yake kuma shine..... ABINDA ZAA NEMA. 1. Kaikayi koma kan mashekiya 2. Garin kusdul hindi 3. Garin haltit Zaa hade wannan waje daya,sai a rika diban kadan ana zubawa akan wuta mara lafiya ya rika shakar hayakin. Idan kuma don kariya zaai kawai sai a saka a daki ko a cikin gida. Wallahu a'alamu Abin sadaqa ayiwa Annabi sallallahu Alaihi wasallam Salati. LIKE AND SHARE.

Tarihin Sayyadina Umar bin Khaddab عمر بن الخطاب, (Allah Ya kara masa yarda):

Shimfiɗa.  Umar bn al-Khaṭṭāb ( RA) shi ne khalifan Rashidun na biyu, wanda ya yi mulki daga watan Agusta 634 har zuwa kashe shi a shekara ta 644. Ya gaji  Sayyidina Abubakar ( RA) a matsayin khalifan Rashidun na biyu a ranar 23 ga Agusta 634. Umar babban sahabi ne kuma surukinsa annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama. Menene Umar Ibn al-Khattab aka sani da shi? Umar babban sahabi ne kuma mashawarcin annabin musulunci Muhammad SAW, kuma ya zama shugaba musulmi na biyu bayan wafatin Muhammad ya kuma yi mulki na tsawon shekaru 10. Ya Musulunta a shekara ta 6 bayan wahayin Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama na farko, ya shafe shekaru 18 yana sahabi Muhammad SAW.  “Da za a samu wani Annabi a bayana, da ya kasance Umar dan Khaddabi ne.”  – Manzon Allah (SAW). Shi ne Umar dan Khaddabi dan Nufailu dan Addi dan Abdul Uzza dan Ribalu dan Abdullahi dan Kurdu dan Razahu dan Addi dan Ka’abu, Bakuraishe, Bamakhzume. Sun hada nasaba da Annabi (SAW). Ana yi masa alku...

SAHABBAI GOMA DA AKA YIWA BUSHARA DA ALJANNA TIN ANAN DUNIYA:-

 *1. Abubakar As-sidiq(R.A) *2. Umar Bin Khattab(R.A) *3. Uthman Bin Affan(R.A) *4. Aliyu Bin Abi-Talib(R.A) *5. Zubair Bin Auwam(R.) *6. Sa'adu Bin Abi Waqas(R.A) *7. Abu Ubaida Bin Jarrah(R.A) *8. Dalhatu Bin Ubaidullah(R.A) *9. Abdurrahman Bin Auf(R.A) *10. Sa'idu Bin Zaid Al-Quraishi(R.A). ♡♡♤♤♡♡♤♤♡♡ ALLAH YA BAMU ALBARKACINSU, ALLAH YA KARA LINKA RAHAMA DA YARDA A GARE SU AMEEEEEN.