A True Life Story!
A garinmu Anyi wasu kishiyoyi guda biyu (2) masu bakaken zuciya, Babu ranar da garin Allah zai waye daga safiya zuwa maraice face Sai sunyi fada (Cacan Baki) ko Kuma dambe.
.
In kuwa kaga haka bai faru ba, to tabbas dayace tayi tafiya ko Kuma rashin lafiya mai tsanani ya kwantar da ita.
.
Lamarin yana matukar damun Maigidansu, yayi duk wani abinda ya dace don ganin kawo karshen wannan badakalar amma kokarinsa bai kai ga matakin cin Nasara ba.
.
WAI ME YASA BAZAI SAKESU BA KAWAI YA HUTA?
.
Wannan shine abinda zaka ji bakunan mutane na furtawa a duk sanda aka tashi batu akan wannan al'amari.
"Ni Kuwa cewa nayi: "Watakila yana saurara musu ne a dalilin 'ya'yansu.
.
Toh amma menene amfanin hakan tunda su ba duba hakan suke yii ba.
Sai dai a madadin duk wannan, Maigidan ya yankewa kansa wani hukunci Wanda yake gani shine daidai dashi, Wannan kuwa ba Komai bane illa daina zuwa gidansa a wasu lokuta na tsawon kwana biyu ko uku tare da cewar yana gari, ba tafiya yayi ba.
.
Wanda hakan kamar kuntatuwane a gareshi,
Ana cikin hakanne, rannan Sai amarya ta zabura kamar wadda aka yiwa allurar soja.
.
Bayan uwar gidanta ta gama abincin dare tana shirye shiryen kintsawa domin dawowan Maigida, Ashe Amarya ta dafa ruwa a stove mai shegen zafi, ta dibi gishiri mai yawa ta afka cikin ruwan zafinnan.
.
Koda uwar gida ta shiga bandaki (Bath room) domin ta yi wanka, can kuwa Sai amarya tabi bayanta, tana shiga Sai ta tarar da 'yar uwar tata (Uwar Gida) a tube harma ta goga sabulu a fuska.
.
Cikin rashin Imani, haka amaryarnan ta Daga ruwan zafi da ta tafi dashi (Wanda yake hade da gishiri) ta kwarawa uwar gidanta a jiki!
.
Uwar gidannan Ta saka salati gami da yin wata kara (Ihu) mai zaburarwa.
.
Kafin kace kobo jama'a sun taru a gidan, Ita kuwa amaryar da taga haka Sai ta ari Na kare.
.
Nan da nan aka sungumi uwar gidannan zuwa asibiti, idan ka ganta ba zaka so ka Kuma ganinta ba "domin ilahirin fatar (skin) jikinta ya salube.
.
Ya dauketa adadin awowi mai yawan gaske kafin ta farfado, kamar yadda ya dauketa adadin watanni mai yawan gaske kafin ta warke. Koda ta warke, haka kamanninta gaba daya ya chanja. Abindai Sai Wanda ya gani.
.
Nasan mai karatu ya zaku yaji ko wani irin mataki Mijin ya dauka akan amaryar, to ba Komai yayi mata ba illa iyaka ya saketa shika uku.
.
Su Kuma iyayen uwar Gida suka ce basu yarda ba Sai anje kotu, amma daga bisani da aka zauna a Gida Sai aka fahimci juna, aka sasanta Kuma aka yafi juna.
Allah ya rabamu da irin wadannan mata, su Kuma Allah ya sauwake musu, Ameen.
Comments
Post a Comment