Skip to main content

ASALIN RUBUTUN HAUSAR BOKO KASHI NA DAYA (1)

Rubuta Hausa a cikin bakaken boko ya samo asali ne tun wajen Karni na 17/18 lokacin da Turawan Mishan da ’yan kasuwa suka rika shigowa Nahiyar Afirka.

Turawan sun yi kokarin sanin harshen Hausa da al’adunsa kamar yadda suka yi a kan sauran harsunan da suka tarar, inda suka rika aika rahotannin abin da suka samu zuwa kasashenmu don a rika bugawa a mujallu da littattfai.

Kuma bincike ya nuna cewa an fara rubuta Hausa a cikin kalmomin boko ne a kasar Denmark a Karni na 18.

Yadda aka fara rubutun Hausar Boko

Sarkin Denmark na lokacin ne ya tura wakilansa zuwa kasashen Larabawa don su yi binciken kimiyya a 1773 Miladiyya, kuma a cikin wadanda ya tura akwai wani Bature mai suna B.G. Niebuhr.

Bayan wannan bincike sai wani Balaraben kasar Tunisiya mai suna Abdurrahman da wani bawansa mutumin Borno da ya ji Hausa suka kai ziyayar jakadanci kasar Denmark.

Niebuhr ya zama tafinta mai fassara tattaunawa a tsakanin Sarkin Denmark da Balaraben nan.

Sai abota ta shiga tsakanin Niebuhr da Balaraben, daga nan Niebuhr ya yi sha’awar koyon Hausa daga wancan bawan Balaraben.

Sakamakon haka B.G. Niebuhr ya dukufa ga koyon Hausa, bawan nan yana gaya masa sunayen abubuwa yana rubutawa da bakaken boko gwargwadon yadda ya ji muryar kalmomin tare da fassararsu.

Amma saboda rashin kwarerwasa a harshen da kuma rashin dokokin rubutun Hausa sai ya zamo bai rubuta kalmomin yadda suka kamata ba.

Wannan ya sa in aka dubi kalmomin da ya rubuta a wancan lokaci za a ga akwai kura-kurai a tsakanin yadda ake furta kalmomin da yadda ya rubuta su a cikin wani littafinsa mai suna: “The Life of Niebuhr” wanda aka buga a kasar Denmark a 1791, wato shekara 229 da suka gabata.

Misali, ga yadda ya rubuta wasu kalmomin:

Kalma    Yana Nufin                Ingilishi 
       
Motum       –      Mutum           –     Man
Koroma     –      Korama           –    Stream
Ghurassa    –     Gurasa             –    Wheaten food
Berni          –     Birni               –     Town
Daua          –     Dawa              –    Guinea corn
Shinkaffer  –     Shinkafa          –    Rice
Sirki           –     Sarki                –    Emir/Chief
Crua          –     Ruwa               –    Water

Bayan Niebur, a cikin Turawa masu ziyarar gano Afirka na farkon Karni na 19 wadanda suka yi rubuce-rubuce da Hausar boko, babu kamar Henric Barth da J.F. Schon.

Henric Barth da Kungiyar gano Afirka

Henric Barth Bajamushe ne da ya jagoranci kungiyar gano Afirka.

Sannan a tsakanin 1850 zuwa 1855 ne lokacin da yake tafiye-tafiyensa a Afirka ya hadu da wadansu samari biyu Dorugu da Abbega.

Dorugu Bahaushe ne haifaffen Damagaram a Jamhuriyyar Nijar, wanda tun yana yaro aka sayar da shi ga wani Balarabe a 1851.

Abbega kuma dan kabilar Margi ne daga Borno/Adamawa.

Henric Barth ya fanshi Dorugu da Abbega daga Balaraben, ya debe su ya tafi da su Tumbuktu a kasar Mali.

Daga nan ya zarce da su zuwa Ingila a 1855 inda suka rika koya masa Hausa suna ba shi labarai.

Sakamakon haka ne Barth ya rubuta wani littafi na musamman kan harsunan Hausa da Filatanci da Barbarci mai suna:

“Collection of Vocabularies of Central African Languages, Gotha 1862.

Yan mishan masu yada Kiristanci

Mista J.F. Schon shi ne gwarzon rubuce-rubuce cikin Hausar boko a Turai kafin Karni na 20.

An haife shi a Jamus a 1803, kuma ya mika kansa ga wata kungiyar yada addinin Kirista mai suna Church Missionary Society (CMS) wadda ta aiko shi kasar Saliyo a 1832 inda ya shekara bakwai yana aikin yada addinin Kirista yana hadawa da koyon harsunan Afirka a wurin ’yantattun bayi.

Schon ya koma Ingila a 1847 ya yi zamansa yana rubuta littattafai kan harshen Hausa da wasu harsunan Afirka.

Yana cikin aikin shi kadansa sai ya ci sa’a ya hadu da samarin nan biyu Dorugu da Abbega wadanda suka bi Henric Barth zuwa Ingila.

Schon ya nemi Barth ya ara masa su don su taimaka masa ya rika nazari kan harshen Hausa.

Barth ya yarje masa suka je wurin Schon suka zauna na shekara takwas suna taimakon sa yana rubuta littattafan Labarai da bayanai da Nahwun Hausa da Kamus na Hausa da kuma fassare-fassaren wasu littattafan addinin Kirista daga Ingilishi zuwa Hausa.

Schon ya rubuta littattafai da dama a kan Hausa wadanda suka zama littattafan yin nazari da koyon Hausa ga Turawa masu son zuwa Afirka.

Kuma wadannan littattafai ne suka zama harsashin gina rubutun Hausa a Karni na 20.

Wasu daga cikin littattafan su ne:

Schon J. F. Address to the Chiefs and People of Africa (in Hausa), Cape Coast, 1841.

Schon J. F. Farawa Letafen Magana Hausa, Berlin, 1857.

Schon J. F. Letafen Musa Nafari B.F.B.S, London 1858.

Schon J. F. Letafen Musa Nabi’u B.F.B.S, London 1858.

Schon J. F. Grammer of the Hausa Language, C.M.S. London, 1862.

Schon J. F. Dictionary of the Hausa Language, C.M.S, London, 1876.

Schon J. F. Hausa Reading Book, C.M.S. London 1877.

Schon J. F. Labari Nagari. C.M.S. London, 1877.

Schon J. F. Letafe No Alwasi Sabo. C.M.S. London 1880.

Schon J. F. Magana Hausa, S.P.C.K. London 1885.

Comments

Popular posts from this blog

Tarihin Sayyadina Umar bin Khaddab عمر بن الخطاب, (Allah Ya kara masa yarda):

Shimfiɗa.  Umar bn al-Khaṭṭāb ( RA) shi ne khalifan Rashidun na biyu, wanda ya yi mulki daga watan Agusta 634 har zuwa kashe shi a shekara ta 644. Ya gaji  Sayyidina Abubakar ( RA) a matsayin khalifan Rashidun na biyu a ranar 23 ga Agusta 634. Umar babban sahabi ne kuma surukinsa annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama. Menene Umar Ibn al-Khattab aka sani da shi? Umar babban sahabi ne kuma mashawarcin annabin musulunci Muhammad SAW, kuma ya zama shugaba musulmi na biyu bayan wafatin Muhammad ya kuma yi mulki na tsawon shekaru 10. Ya Musulunta a shekara ta 6 bayan wahayin Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama na farko, ya shafe shekaru 18 yana sahabi Muhammad SAW.  “Da za a samu wani Annabi a bayana, da ya kasance Umar dan Khaddabi ne.”  – Manzon Allah (SAW). Shi ne Umar dan Khaddabi dan Nufailu dan Addi dan Abdul Uzza dan Ribalu dan Abdullahi dan Kurdu dan Razahu dan Addi dan Ka’abu, Bakuraishe, Bamakhzume. Sun hada nasaba da Annabi (SAW). Ana yi masa alku...

MAGANIN KARYA SIHIRI(HAYAKI)

 Alhamdulillah kamar yadda mukai Alkawarin zamu kawo maganin wanda yake karya sihiri ko jifa,ko sammu Allah ya nufa yau mun cika shi. Kuma shi wannan na hayaki ne wanda mutum zai hada ya rika zuba shi akan garwashi yana amfami dashi,yadda abun yake kuma shine..... ABINDA ZAA NEMA. 1. Kaikayi koma kan mashekiya 2. Garin kusdul hindi 3. Garin haltit Zaa hade wannan waje daya,sai a rika diban kadan ana zubawa akan wuta mara lafiya ya rika shakar hayakin. Idan kuma don kariya zaai kawai sai a saka a daki ko a cikin gida. Wallahu a'alamu Abin sadaqa ayiwa Annabi sallallahu Alaihi wasallam Salati. LIKE AND SHARE.

SAHABBAI GOMA DA AKA YIWA BUSHARA DA ALJANNA TIN ANAN DUNIYA:-

 *1. Abubakar As-sidiq(R.A) *2. Umar Bin Khattab(R.A) *3. Uthman Bin Affan(R.A) *4. Aliyu Bin Abi-Talib(R.A) *5. Zubair Bin Auwam(R.) *6. Sa'adu Bin Abi Waqas(R.A) *7. Abu Ubaida Bin Jarrah(R.A) *8. Dalhatu Bin Ubaidullah(R.A) *9. Abdurrahman Bin Auf(R.A) *10. Sa'idu Bin Zaid Al-Quraishi(R.A). ♡♡♤♤♡♡♤♤♡♡ ALLAH YA BAMU ALBARKACINSU, ALLAH YA KARA LINKA RAHAMA DA YARDA A GARE SU AMEEEEEN.