Zuriyar Harshen Hausa Masana ilimin harsuna sun karkasa harsunan duniya zuriya-zuriya. Kowane harshe na duniyar mutane dole da rukunin da yake. A rukunin da ya fito nan ake kirdadon tushensa da tushen masu magana da shi. Masana ilimin harshe sun ce: Hausa harshe ne daga cikin zuriyar harsunan Chadi, waɗanda sun kai fiye da harsuna ɗari da ake magana da su a Arewacin Najeriya da Arewacin Kamaru da kuma tsakiyar Chadi.” Daga cikin harsuna iyalan Chadi, Hausa ta fi kowane bazuwa da yawan jama’a da karɓuwa da mamaye ƙasa. Daga cikin fahimtar sanin asalin harshe shi ne a san tarihinsa. Babban muhimmin abu shi ne gano dangantakar harshe da sauran harsunan da suke zuriya/iyali ɗaya. Babu makawa ga mai son sanin tushen Hausa ya yi ƙwaƙƙwaran nazarin harsuna iyalan Chadi. A tsarin ilimin harsuna an ce: Idan aka ce harshe (kaza) ɗan iyalan gungun harsuna (kaza) ne, ana son a tabbatar da cewa, a da can baya harshe ɗaya ne kacal daga gare shi ne sauran harsunan zuriyarsa suka tsir...
Rubuta Hausa a cikin bakaken boko ya samo asali ne tun wajen Karni na 17/18 lokacin da Turawan Mishan da ’yan kasuwa suka rika shigowa Nahiyar Afirka. Turawan sun yi kokarin sanin harshen Hausa da al’adunsa kamar yadda suka yi a kan sauran harsunan da suka tarar, inda suka rika aika rahotannin abin da suka samu zuwa kasashenmu don a rika bugawa a mujallu da littattfai. Kuma bincike ya nuna cewa an fara rubuta Hausa a cikin kalmomin boko ne a kasar Denmark a Karni na 18. Yadda aka fara rubutun Hausar Boko Sarkin Denmark na lokacin ne ya tura wakilansa zuwa kasashen Larabawa don su yi binciken kimiyya a 1773 Miladiyya, kuma a cikin wadanda ya tura akwai wani Bature mai suna B.G. Niebuhr. Bayan wannan bincike sai wani Balaraben kasar Tunisiya mai suna Abdurrahman da wani bawansa mutumin Borno da ya ji Hausa suka kai ziyayar jakadanci kasar Denmark. Niebuhr ya zama tafinta mai fassara tattaunawa a tsakanin Sarkin Denmark da Balaraben nan. Sai abota ta shiga tsakanin Niebuhr da ...