Skip to main content

MUNA SON AYI MANA UZURI AMMA BA SON YI WA WASU UZURI.

 

Talakawan Nigeria muna tashi da wani Mentality wanda yana daga cikin abinda ke kawo mana gaba da kiyayyar junanmu. Misali:

1. Idan Dan siyasa ya gina makarantar kudi sai mu ke zaginsa wai ya kamata ya sanya makarantar ta zama kyauta. Shin idan Dan siyasa bai yi abubuwan da za su kawo masa kudi ba so mu ke ya ke satar kudinmu?

2. Idan muna da alaka da wani mai kudi, idan muka je sayen kayansa musamman idan kayan ba su da yawa sai mu ke tunani ya kamata mai kudin ya ba mu kayan ya ce mu bar kudin. Inda kuma aka yi sa'a mai kudin ya karbi kudin kayan sai mu ce ba shi da mutunci. Shin idan ba neman kudi ya ke ba mai ya sa ya ke sayar da kayan? Idan zai dinga ba mu kaya kyauta shi kuma a ina za'a ke bashi kaya kyauta?

3. Kuskuren da kusan kowa ya ke yi, idan Malami ya yi sai ya zama abin yayatawa. Shin dama tunani mu ke su Malamai wasu mutane ne daban da yadda mu ke? Idan har kana da zuciya to su ma suna da ita, yadda ka ke da sha'awa haka su ma suna da ita, yadda ka ke jin fushi to suma suna yin fushi, yadda ka ke son jin dadi su ma fah suna son jin hadin.

4. Muna zabar Gwamna, Senator, Rep, Member da Chairman, amma dukkanin aikin da wadannan za su yi muna dorawa Shugaban kasa ne. Shin idan shugaban kasa ne zai yi kowanne aiki mai ya sa mu ke zaben wasu kujerun?

5. Idan wani Dan kasuwa da ke yankinmu ya tafi wani yankin ko Kasar waje ya gina kamfani sai mu ce ba shi da kishinmu har mu dinga zaginsa. Shin kishin gari shi.

Comments

Popular posts from this blog

Tarihin Sayyadina Umar bin Khaddab عمر بن الخطاب, (Allah Ya kara masa yarda):

Shimfiɗa.  Umar bn al-Khaṭṭāb ( RA) shi ne khalifan Rashidun na biyu, wanda ya yi mulki daga watan Agusta 634 har zuwa kashe shi a shekara ta 644. Ya gaji  Sayyidina Abubakar ( RA) a matsayin khalifan Rashidun na biyu a ranar 23 ga Agusta 634. Umar babban sahabi ne kuma surukinsa annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama. Menene Umar Ibn al-Khattab aka sani da shi? Umar babban sahabi ne kuma mashawarcin annabin musulunci Muhammad SAW, kuma ya zama shugaba musulmi na biyu bayan wafatin Muhammad ya kuma yi mulki na tsawon shekaru 10. Ya Musulunta a shekara ta 6 bayan wahayin Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama na farko, ya shafe shekaru 18 yana sahabi Muhammad SAW.  “Da za a samu wani Annabi a bayana, da ya kasance Umar dan Khaddabi ne.”  – Manzon Allah (SAW). Shi ne Umar dan Khaddabi dan Nufailu dan Addi dan Abdul Uzza dan Ribalu dan Abdullahi dan Kurdu dan Razahu dan Addi dan Ka’abu, Bakuraishe, Bamakhzume. Sun hada nasaba da Annabi (SAW). Ana yi masa alku...

MAGANIN KARYA SIHIRI(HAYAKI)

 Alhamdulillah kamar yadda mukai Alkawarin zamu kawo maganin wanda yake karya sihiri ko jifa,ko sammu Allah ya nufa yau mun cika shi. Kuma shi wannan na hayaki ne wanda mutum zai hada ya rika zuba shi akan garwashi yana amfami dashi,yadda abun yake kuma shine..... ABINDA ZAA NEMA. 1. Kaikayi koma kan mashekiya 2. Garin kusdul hindi 3. Garin haltit Zaa hade wannan waje daya,sai a rika diban kadan ana zubawa akan wuta mara lafiya ya rika shakar hayakin. Idan kuma don kariya zaai kawai sai a saka a daki ko a cikin gida. Wallahu a'alamu Abin sadaqa ayiwa Annabi sallallahu Alaihi wasallam Salati. LIKE AND SHARE.

SAHABBAI GOMA DA AKA YIWA BUSHARA DA ALJANNA TIN ANAN DUNIYA:-

 *1. Abubakar As-sidiq(R.A) *2. Umar Bin Khattab(R.A) *3. Uthman Bin Affan(R.A) *4. Aliyu Bin Abi-Talib(R.A) *5. Zubair Bin Auwam(R.) *6. Sa'adu Bin Abi Waqas(R.A) *7. Abu Ubaida Bin Jarrah(R.A) *8. Dalhatu Bin Ubaidullah(R.A) *9. Abdurrahman Bin Auf(R.A) *10. Sa'idu Bin Zaid Al-Quraishi(R.A). ♡♡♤♤♡♡♤♤♡♡ ALLAH YA BAMU ALBARKACINSU, ALLAH YA KARA LINKA RAHAMA DA YARDA A GARE SU AMEEEEEN.