Talakawan Nigeria muna tashi da wani Mentality wanda yana daga cikin abinda ke kawo mana gaba da kiyayyar junanmu. Misali: 1. Idan Dan siyasa ya gina makarantar kudi sai mu ke zaginsa wai ya kamata ya sanya makarantar ta zama kyauta. Shin idan Dan siyasa bai yi abubuwan da za su kawo masa kudi ba so mu ke ya ke satar kudinmu? 2. Idan muna da alaka da wani mai kudi, idan muka je sayen kayansa musamman idan kayan ba su da yawa sai mu ke tunani ya kamata mai kudin ya ba mu kayan ya ce mu bar kudin. Inda kuma aka yi sa'a mai kudin ya karbi kudin kayan sai mu ce ba shi da mutunci. Shin idan ba neman kudi ya ke ba mai ya sa ya ke sayar da kayan? Idan zai dinga ba mu kaya kyauta shi kuma a ina za'a ke bashi kaya kyauta? 3. Kuskuren da kusan kowa ya ke yi, idan Malami ya yi sai ya zama abin yayatawa. Shin dama tunani mu ke su Malamai wasu mutane ne daban da yadda mu ke? Idan har kana da zuciya to su ma suna da ita, yadda ka ke da sha'awa haka su ma suna da ita, yadda ka ke jin fu...