Shin ko kasan yanda Muqabalar Alkali Abubakar Al-Baqillaniy a kan Annabi Isa (as) a Fadar Paparoma ta Gudana?
Paparoma ya ji Fada ya nuna akwai matsala a cikin maruwaitar Mu'ujizar tsagewar wata ga Annabi Muhammad (saw), har ya ji dadi, ya samu kofar sukar Mu'ijizar Annabi (saw), shi ya sa ya tambayi Fadan, ta yaya za a soki maruwaita Mu'ijizar ta tsagewar wata? Sai Fada ya ce: Irin wadannan Mu'ujizozi in da a ce sun inganta, to dole a ce mutane masu yawa ne suka ruwaito daga wasu mutanen masu yawa, haka har ya iso gare mu. Da a ce haka ya faru da dole mu san hakan ya faru. Amma tun da hakan bai faru ba, to wannan yana nuna cewa; kawai karya ce aka kirkira. Sai Paparoma ya juya ya fiskanci Alkali Abubakar Al-Baqillaniy, ya ce: To kawo amsa. Sai Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya ce: To ai abin da kuka fada a kan tsagewar watan irinsa zan fada a kan "Ma'ida" da aka saukar wa Annabi Isa (as) daga sama. Sai a ce muku: Da a ce da gaske an saukar wa Annabi Isa (as) "Ma'ida" daga sama to dole a ce mutane masu yawa ne suka ruwaito daga wasu mutanen su...